Honorabul Adamu Ahmad Dattijo ya bayyana cewar kulle boda da shugaba Buhari yayi babu abinda ya haifarwa yankin arewacin kasar nan illa tabarbarewar tattalin arziki yankin da tsadar rayuwa. Hon Adamu Dattijo ya bayyana hakan ne a shirin Dialogue da ake gabatarwa a gidan talbijin na liberty TV dake Kaduna.
” Dattijo yace ko rufe boda da shugaba Buhari yayi, yayi shi ne kawai domin ya karya yankin arewacin kasar nan, domin mafi yawancin matasan yankin arewacin kasar nan sun rasa ayyukan su ba tare da gwamnati ta bullo masu da wasu hanyoyin ba.kuma a lokaci daya gwamnati ta bar tekun yankin kudancin kasar nan domin samun haraji mafi tsoka wanda hakan kadai yasa rayuwa tayi tsada a yankin arewa.
Shugaba Buhari yace zasu bude iyakokin kasar nan biyo bayan shawarwarin da masana tattalin arziki suka ba gwamnati na ganin an bude bodar domin samun farfado da tattalin arzikin kasar da ya kamo hanyar durkushewa.
Hon Adamu Dattijo yace idan ka zauna ka lissafa koda gwamnati tace a koma gona, tsakanin manoman mu da masu kanfanin gyara shinkafar waye yafi samun albarkacin rufe boda?
Domin manyan masu kanfanonin nan suke anfana da tsarin rashin shigo da shinkafar ketare domin sune gwamnati ke taimakawa da manyan kudaden tallafi bawai talakan dake noma a gonar sa ba. Yanzu masu kanfanin nan suke zuwa kauyakun mu daga kudancin kasar nan suna siyan abincin a arhar banza, sukai kanfanonin su kuma suzo suna siyar mana da tsada. Domin yanzu shinkafar da ake nomawa kasar tafi karfin talaka, saboda a kasuwa ma sai kana da naira dubu 25 zuwa 30 zaka samu shinkafar gida.
Kamin a rufe mana boda muna samun abinci cikin sauki kuma fa kawo mana shi kasar nan ake yi bayan biyan haraji da kudin jigilar sa daga wani kasa. Shi kuma wanda ake nomawa a kasar mu najeriya ba tare da anyi jigilar sa daga wata kasa ba, kuma ba tare da anbiya haraji ba kuma yafi wanda ake shigo mana dashi tsada. To Dan Allah ina anfanin rufe boda ga talakan arewa a irin wannan hali?
Shin kun yarda da ra’ayin Hon Adamu Dattijo musamman ganin cewa yanzu gwamnati ta dawo kuma zata bude bodar a halin yanzu ganin yadda rayuwa take kara tsada a fadin kasar nan?
Ku cigaba da binmu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su.

