Rahotannin dake shigo mana daga jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar ya bukaci mazauna yankin da aka kai wa hari kwanan nan a karamar hukumar Alkaleri da su tashi su dauki makamai su kare kansu daga yan bindigar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a fadar Hakimin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri a ziyarar da ya kai kauyen Rimi, Gwana da Yalwan Duguri domin jajanta wa wadanda yan fashin suka kai wa hari.
Ya ce lamarin wani hanyar da ba za a amince da ita ba ne wanda dole ne a dakatar da shi ko ta yaya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Gwamnan ya shawarci jamaa da su kamo mugayen baragurbi tare da hada kai da yan bindigar, musamman wadanda ke aiki a matsayin masu ba da labari, inda ya kara da cewa masu laifin ba za su iya yin aiki ba tare da wasu a cikinku ba.
Da yake mayar da martani, Hakimin Yelwa Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya ce mutane 20 ne aka kashe a kauyen Rimi a lokacin hare-haren kuma yunkurinsu na kaiwa Kafin Duguri ya ci tura yayin da mutanen kauyen suka tashi domin kare kauyen.

