Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun Koli ta yi watsi da karar da PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka zuwa gabanta ta neman soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa na jam’iyyar APC.
A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar yau Juma’a ta ce PDP ba ta da dama a doka ta yi kara a kan lamarin saboda a cewar kotun PDP ba mamba ce ta jam’iyyar APC ba.
Masu korafin suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Tinubu ya saba wa sassa na 29(1), 33, 35, da kuma na 84(1)(2) na doka zabe ta kasar ta 2022.
A karar suna cewa Shettima ya saba doka saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.
A don haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar APC da Tinubu da Shettima daga takarar wadda suka riga suka yi ta zaben shugaban.
Hukuncin kotun kolin ya kasance daidai da wanda wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi tun da farko.

