Wata babbar kotu da ke Kubwa a Abuja, ta umarci Alhaji Atiku Abubakar da ya mayar wa Maryam Sherif, tsohuwar matarsa yaransu 3 da ke hannunsa take-yanke.
A shekarar da ta gabata ne Maryam Shereef ta maka Abubakar kotu, inda take bukatar ya bata yaransu maza 3 da yake rike dasu.
Abubakar ?a ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Alkalin kotun, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai bayar da wata hajja a musulunce da za ta hana uwar amsar yaranta ba.
Amma zai iya daukaka kara cikin kwanaki 30. A kotun, Maryam da lauyanta, Nasir Sa’idu sun halarci zaman, yayin da Abubakar da lauyansa , Abdullahi Hassan kuwa basu je ba.

