Site icon Muryar 'Yanci

Kotu Ta Sanya Ranar Saurarar Bukatar Mi?a Kyari Amurka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Kotun tarayya dake zamanta a birnin ta za?i ranar 23 ga watan Maris, 2022 domin fara tafka mahawara kan bukatar gwamnatin tarayya na mi?a Abba Kyari zuwa Amurka.

An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ofishin Antoni Janar na ?asa, Abubakar Malami, ta shigar da bukatar gaban Kotu, ?ara mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022. Karar wacce aka ra?a wa, “Neman sahalewar mi?a Abba Kyari ga ?asar Amurka,” na ?auke da kwanan wata dai-dai da ranar da aka shigar da ita 2 ga watan Maris.

Haka nan kuma, Antoni Janar shi ne wanda ya shigar da ?arar, yayin da mataimakin kwamishinan yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ne ake neman umarnin Kotun a kansa.

An shigar da bukatar ne karkashin dokar mi?a dan ?asa a wani bangare na amincewar da gwamnatin Najeriya ta yi wa bukatar Amurka na mi?a mata Abba Kyari.

Gwamnati ta tura bukatar ne kai tsaye ga shugaban Alkalai, tare da masa bayanin cewa bukatar ta fito ne daga ofishin diflimasiyya na ofishin jakadancin Amurka a Abuja.

Exit mobile version