Kotun ?olin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin ku?in ?asar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ?asa ya bayar da umarnin sake fasalin ku?in da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.
Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.
Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ?olin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin ku?in ?asa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.
Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.
Tun da fari gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar da gwamnati ?ara, kuma ?arar da suka shigar aka yi amfani da ita a matsayin hujja wajen yanke wannan hukunci.
A watan jiya kuma wasu gwamnoni suka ?ara bin bayansu wajen shigar da ?arar, abin da ya janyo kotun ?olin ta dakatar da waadin na wucin gadi da aka sanya na daina amfani da tsofaffin ku?in.

