Site icon Muryar 'Yanci

Kotu Ta Haramta Wa ‘Yan Jarida Halartar Shari’un ‘Yan Ta’adda

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Alkalin alkalan babbar kotun tarayya John Tsoho ya fitar da wata sanarwa da ke bayyana yadda kotun za ta rika gudanar da shari’un da suka jibanci ta’addanci a gaban kotun.

Akwai shari’un da ke gaban kotun, ciki har da wanda ake wa Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci da ta ‘yan canjin kudi da ake tuhuma da taimaka wa ‘yan ta’adda, da kuma mayakan Boko Haram.

Alkali Tsoho ya ce sababbin tsare tsaren gudanar da ayyukan kotun na karkashin dokar kasa a karkashin sashe na 254 na tsarin mulkin Najeriya 1999.

Sanarwar ta ce a karkashin wannan sabon tsarin, za a hana kafafen yada labarai halarta da yin rahotanni kan shari’un, sai dai idan kotun ta amince da haka.

Exit mobile version