Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara waadin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu.
Alkalin kotun, Mai Sharia Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara waadin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki.
Da yake sauraron ?arar da wasu biyar daga cikin jamiyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci shugabannin bankuna da jamiansu su kawo dalilan da za su hana a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin su da yin zagon kasa ga tattalin arziki, bisa yadda suke boye sabbin takardun Naira 1,000 da N500 da kuma N200

