Site icon Muryar 'Yanci

Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Rufe Layukan Wayoyin ‘Yan Najeriya

Gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa na ?asar nan zasu tattauna da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa kan hukuncin da kotu ta yanke na hana gwamnati rufe layukan da ba’a ha?a su da katin ?an ?asa (NIN) ba daga ranar 6 ga watan Afrilu.

A ranar Laraba wata babbar kotun tarayya dake Lagos ta hana gwamnati rufe layukan da ba’a ha?asu da NIN ba a watan Afrilu.

Jami’an ma’aikatar sadarwa da ma’aikatan kamfanonin sadarwa sun tabbatar da cewa ana samun cigaba sosai na masu yin NIN da kuma ha?a shi da layukan waya. Sun kuma ?ara da cewa za’a duba hukuncin da kotu ta yi na hana rufe layukan waya a watan Afrilu. Za’a yi taro tsakanin ?angarorin dake da alhaki kan lamarin don duba hukuncin na kotu kafin wa’adin 6 ga watan Afrilu ya cika.

Tsohon mataimakin shugaban ?ungiyar lauyoyi ta ?asa,, kuma lauyan kare hakkin bil’adama, Monday Ubani, ne ya shigar da ?ara gaban kotu.

Ya nemi kotun da ta hana gwamnati rufe layukan mutane wa?anda ba’a ha?a su da NIN ba a watan Afrilu kamar yadda take shirin yi.

Daga cikin wa?anda ya shigar ?arar akwai; Al?alin Al?alai na ?asa, hukumar kula da harkokin sadarwa NCC, da kuma ma’aikatar sadarwa wadda Pantami ke jagoranta.

“Wa?annan sune abubuwan da za’a tattauna a taron da za’ayi kafin wa’adin ya cika ranar 6 ga watan Afrilu,” a cewar wani ma’aikacin sadarwa wanda ya nemi a ?oye sunansa.

Ma’aikacin yace, Shugaban ?ungiyar kamfanonin sadarwa, Ikechukwu Nnamani, shi zai yanke lokacin da za’a yi taron nan gaba. Ya kuma ?ara da cewa, ministan sadarwa, Isa Pantami, shi zai bayyana ma mutane hukuncin da gwamnati ta yanke kan wa’adin 6 ga watan Afrilu bada jimawa ba.

Exit mobile version