Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta ba hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), umarni da ta tabbatar da shugaban ?ungiyar ?an a-waren Biafra Nnamdi Kanu ya samu cikakkiyar walwala yayin da yake tsare a hannunsu.
Wannan umurni ya biyo bayan ?orafin da lauyoyinsa suka yi na cewa wanda suke karewa an hana shi walwala ko canza kaya da yin addininsa ba ya iya wa a yayin da yake tsare.
Sauraren shariar gaggawar da aka yi ya zo bayan tsegwamin da lauyoyinsa suka yi cewa ?age shariar da aka yi tun da farko ya sa?awa sauraren shariar cikin hanzari da aka shirya yi wa shugaban na IPOB.
Kanu wanda ake tuhuma da cin amanar ?asa bai halarci zaman kotun ba a ranar Alhamis. An ?age shariar zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2022.

