Shugaban darikar katolika na mabiya addinin Kirista, Fafaroma Francis ya fito ya soki harin da yan taaddan Boko Haram su ka kai a jihar Borno, tare da yin Allah wadai da la’antar ayyukan ?ungiyar.
Babban limamin na Rome ya soki harin taaddancin ne a hudubar da ya saba yi a kowane mako a fadarsa dake Vatican.
Ina so in tabbatar da addua ta ga Najeriya, inda cikin takaici, aka sake zubar da jini a harin taaddanci.
Fafaroma ya kira abin da ya auku a garin Zabarmari, jihar Borno, kisan gilla daga yan Boko Haram da ke tada kayar baya.
Shugaban Katolikawan ya yi wa wadanda aka kashe adduar samun rahamar Ubangiji, sannan ya yi wa iyalan da su ka bari addu’a, sannan ya roka wa yan taaddan tuba.
Mu na rokon Ubangiji ya yi masu kyakkyawar tarba cikin aminci, Ya ba danginsu dangana, Ya canza zuciyar wadanda su ke taadin da ke bata masa suna.
A wannan harin, yan taaddan sun karkashe manoman ta hanyar yanka wuyayansu a cikin gonaki.
Maganar Fafaroman ta zo ne kwanaki bayan yan taaddan sun shiga har gonakin wasu Bayin Allah fiye da 40, sun yi masu yankan rago a ?auyen Zabarmari dake yankin ?aramar Hukumar Jere a jihar Borno.

