Site icon Muryar 'Yanci

Kisan Manoma: Rundunar Soji Ta Cire Kwamandan Ya?i

Mahukunta a sashen rundunar soji dake ya?i da ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno sun cire Kwamandan Bataliyar Soji da aka jibge a Zabarmari da ke yankin karamar hukumar Jere a jihar Borno, biyo bayan kisan gillar da aka yi wa Manoma 43 a yankin.

A ranar asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ?an Boko Haram sun shiga ?auyen Zabarmari, sun bi manoma har gonakinsu tare da hallakasu ta hanyar yi musu yankan rago.

Zabarmari kauye ne mai nisan kilomita 20 kacal daga hedikwatar rundunar atisayen Lafiya Dole wacce ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno. An jibge bataliyar soji ta 195 a yankin Zabarmari domin mayar da martanin gaggawa a lokutan harin mayakan kungiyar Boko Haram.

Sabon Kwamandan da aka tura zai jagoranci binciken neman gawar saura manoma da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka a gonakinsu na shinkafa.

Majalisar dinkin duniya anata ?angaren ta rawaito cewa a kalla mutane 110 aka kashe, lamarin da ke nuni da cewa an samu karuwar adadin mutanen daga 43 da rahotannin farko suka fara sanarwa.

Ana zargin cewa bayan kisan manoman, mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mata ma su yawa.

“Wannan shine hari mafi girma da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula a cikin shekarar nan.Miyagun ‘yan ta’addan sun daure manoman kafin su yankasu, sannan sun kone gonakin manoman da kayan amfanin da aka noma.

Batun kisan ya hasala jama’a, lamarin da yasa da dama suka yi kira a kan gwamnati ta rubanya kokarinta na kawo karshe ayyukan ta’addanci a arewacin Najeriya.

A cikin sakon alhinin kisan manoman da ya fitar ta hannun kakakinsa, shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya “ta ba hukumomin tsaro dukkan abin da suke da bukata domin kare kasa da jama’arta a duk inda suke.”

Exit mobile version