Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa masu ibada a wani cocin katolika na St Francis a garin Owo a jihar Ondo.
Shugaban ya ce ma?iya ne kawai za su aikata wannan mummunan aikin, yana mai cewa za su fuskanci ba?in cikin duniya da na lahira.
Shugaba Buhari ya jajanta wa iyalan wa?anda aka kashe da cocin Katolika da gwamnatin jihar Ondo, inda ya bu?aci hukumomin agajin gaggawa su kai ?auki ga wa?anda suka jikkata.
?an bindigar sun afka cocin ne a ranar Lahadi, suka bu?e wuta, bayanai sun ce an kashe mutane da dama tare da sace wasu da ba a san adadinsu ba.

