Gwamnatin Nijeriya ta sanya hawa jirgin ?asa kyauta sabo da Kirsimeti
Gwamnatin taraiya ta sanar da cewa ?an ?asa za su hau jirgin ?asa kyauta daga 24 ga watan Disambar da mu ke ciki zuwa 4 ga Janairu, 2022.
Manajan Darakta na Hukumar Kula da Harkokin Jirgin ?asa, Fidet Okhiria ne ya baiyana hakan a wata ganawa da ya yi da Kanfanin Daillancin Labarai na ?asa, NAN a yau Juma’a a Abuja.
Ya cean ?auki matakin ne domin saukakawa ?an ?asa su yi zirga-zirga a lokutan bikin Kirsimeti.
“Mu na kira ga fasinjoji da su je su kar?i sahihin tikiti a guraren da su ka dace.
“Mu na kira ga fasinjoji da su bi ?a’idojin kariya da ga kamuwa da korona ta hanyar sanya takunkumin fuska,” in ji shi.

