Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta bayyana Godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa kafa maaikatar kula da dabbobi.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Baba Othman-Ngelzarma ya fitar a Yau Talata a Abuja, ya bayyana cewa kafa maaikatar zai samar da damar sanaar kiwo a fadin ?asar.
Bugu da kari, ya bayyana cewa maaikatar ta kudiri aniyar samar da ingantattun guraben ayyukan yi masu inganci a duk fadin tsarin kimar dabbobi da nufin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Yace, Da wannan ci gaban, MACBAN ta yi imanin cewa, fatan makiyayan Najeriya ya samu nasara a karkashin shirin sabunta fata.
Alkawarin da shugaba Tinubu ya yi, na inganta ayyukan noma na Najeriya don tabbatar da samar da abinci yana cika.
A madadin Shugaba da mambobin kwamitin amintattu na Kungiyar MACBAN, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Saad Abubakar III, da daukacin yayan kungiyar Cattle Breeders ta Nijeriya a fadin ?asar nan suna taya shugaban kasa Kuma babban kwamandan kungiyar murna. Sojojin Najeriya don Samar da wannan gagarumin ci gaba.”

