Rahotanni daga birnin Mina na Jihar Neja na bayyana cewar ?an sanda sun kama wasu mutum 259 da ake zargi da fashin daji da fya?e da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar cikin watan Agusta.
Kwamishinan ?an sanda a jihar, Mista Monday Kuryas ya shaida wa kamfanin dillancin labari na NAN cewa an aikata laifuka a kananan hukumomi 25 na jihar.
Ya bayyana cewa rundunar ?an sanda ta gano bindigogi da harsasai a hannun masu laifin.
Mista Monday ya ce cikin mutanen 259 da ake zargi, an gurfanar da 119 a gaban kotu.
Ya kuma ce an umarci manyan jami’an ?an sanda da ke kananan hukumomin 25 da aka fi aikata laifuka su ?arfafa tsaro a yankunansu.
Sannan ya bu?aci al’ummar jihar da su taimaka wa jami’an tsaro wajen ba su bayanan sirri da kuma kai rahoton duk wani da ba a amince da shi ba.

