Ministan cikin gidan Faransa ya kaddamar da wani ku?iri na rufe wani Masallacin har na tsawon watanni shida saboda irin waazi na tsattsauran ra’ayi da limamin masallacin ke yi.
Gerald Darmanin ya shaida wa tashar talabijin ta Cnews cewa ya gabatar da tsarin rufe masallacin da ke Beauvais, wani gari mai tazarar kilomita 100 daga arewacin birnin Paris, saboda waazin da ba a yarda da shi ba.
Ya ce limamin Masallacin ya mayar da hankali kan Kiristoci da ?an luwa?i da ma?igo da Yahudawa a cikin hu?ubarsa.
Hukumomin Oise, yankin da masallacin yake sun ce tuni suka sanar da cewa sun fara tunanin rufe masallacin saboda waazin da suka ce na tunzurawa ne da rikici da kuma kare jihadi.
Wani jamii ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa tuni aka aika da sanarwar matakin rufe masallacin.
Wata jaridar yankin Courrier Picard ta ruwaito cewa limamin masallacin bai dade da musulunta ba.
Ta ambaci wani lauya na kungiyar da ke kula da masallacin da ke cewa tuni aka dakatar da limamin daga limanci.

