An fuskanci wata takaddama a tsakanin masu zanga-zanga da jamina yansanda a Tel Aviv babban birnin Israila a dai dai lokacin da ake ci gaba da fafata yaki a Gaza.
Yan sandan Israila sun tsare wani mutum a yayin wata zanga-zangar neman sabon zabe, tare da nuna takaicin gazawar gwamnatin kasar wajen kubutar da daukacin mutanen da ke garkame a zirin Gaza.
Hakanan a wani bangare kuma ‘Yan sandan sun kakkama wasu masu zanga-zanga a birnin Tel Aviv, wadanda suka yi kira da firaminista Benjamin Netanyahu ya yi murabus da kuma gudanar da zabe da wuri a yayin da Isra’ila ke ci gaba da barin wuta a Gaza.

