Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Kebbin Argungu Alhaji Mohammed Mera, a ranar 25 ga watan Satumba za nada ministan ya?a labarai da al’adu Lai Mohammed da babbar sarautar Kakakin Kebbi.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da Tsangayar karamci da yawon bude ido, NIHOTOUR, a ranar Juma’a a Abuja ta fitar, wacce ta samu sa hannun Ahmed Sule, daraktan yada labarai da hulda da jama’a.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar 7 ga watan Maris, 2020, yace Sarkin ya baiwa Lai Mohammed Kakakin Kebbi, ma’ana jakadan al’adu na Kebbi domin yaba kwazo na ministan.
Sarkin ya sanar da bada sarautar ga Ministan a Abuja yayin kaddamar da jerin shirye-shiryen na gasar kamun kifi na Argungun na 2020 wanda aka yi daga 11 ga watan Maris zuwa 14.
Sule yace shirye-shiryen sun yi nisa domin nada ministan wannan babbar sarautar, Hukuncin nada Mohammed sarautar daga masarautar Argungun kamar yadda yace, an kai ga matsaya ne bayan taron da aka yi na masarautar tare da duba kokarin ministan wurin tabbatar da bayyanar al’adun Najeriya ga duniya.
Kamar yadda takardar tace, nadin ministan a matsayin Kakakin Kebbi yana daga cikin jerin shagalin wannan shekarar na World Tourism Day wanda gwamnatin jihar Kebbi za ta dauka nauyi a ranar 27 ga watan Satumba.

