Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kebbi na bayyana cewar Mutane hudu yan gida guda ne suka nutse a hatsarin kwale-kwale a yankin Yawuri.
Mazauna yankin sun ce wa?anda hatsarin ya rutsa da su suna hanyarsu ta zuwa gona tsallaken rafi a lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife sakamakon iska mai ?arfin gaske.
Musa Labaran Mahaifin wa?anda hatsarin ya rutsa da su ya shaida wa BBC cewa an samu gawar ?a?ansa hudu yayin da ake ci gaba da neman gawar mutum na biyar da ba a gani ba.
A watan Mayun shekarar da ta gabata, sama da mutum 100 ne suka nutse a ruwa lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a jihar ta Kebbi.
Ana danganta irin wannan alamari ne da yadda ake loda wa kwale-kwale kaya da mutane da suka wuce ?ima da rashin kula da jiragen na ruwa da kuma rashin kyawun yanayi.

