Site icon Muryar 'Yanci

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Tada ?auyuka Takwas A Karamar Hukumar Faskari

Akalla kauyuka takwas ne, da ke cikin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, a halin yanzu babu Kowa a cikin garuruwa, sakamakon hare haren yan bindiga da suka addabi yankin ba dare ba rana, sai an kawo masu hari an kashe mutane da sace da kuma sace masu dukiyoyi, suka yanke shawarar barin garuruwan na su, inda suka fantsama cikin birane.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa wakilinmu ta waya waya cewa maganar gaskiya Muna cikin matsanancin matsalar tsaro, ba dare ba rana, kusan kullum sai an kawo mana hari ko a kashe ko an Sace mutum ko raunata mutum. Shi yasa muka yanke shawarar barin garuruwan mu na haihuwa. Ko ranar juma’a da ta gabata sun zo Kauyen Shuwaki, Muna cikin Sallah juma’a, da mashina, wasu har kayan agaji suka sanyo inda suka kashe mutane goma sha daya nan take har lahira, sun tafi da limamin garin da wasu mutane ko jiya sun bugo waya akai kudin fansa miliyan goma, sun je garin Jar Kuka, inda aka sace mutane goma sha bakwai.

Ya cigaba da cewa zuwa yanzu haka wadannan garuruwa sun zama kufai, duk al’umma garin sun tashi, babu kowa, sun yi gudun hijira Faskari ko Tsafe ta jihar Zamfara sun bazu, akwai Shuwaki inda suka kashe goma sha daya da sace sha daya da Shuwaki Tudun da Gidan Mai Jakkai da Unguwar Gago da Gidan Na Gwamma da Gidan Mai Tadele da Gidan Sa’ida da Sabon Gida da kuma Ruwa Kusa. Wadannan garuruwa da na lissafo ma ba kowa a ciki, duk wanda ya je Sai dai ko zai yo wani abu. Sojoji sun taba zuwa sau daya a yankin, a taimaka a kara mana jami’an tsaro a wannan yankin,

Exit mobile version