‘Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari a kauyen Kaigar Malamai da ke karamar hukumar Danmusa, a jihar Katsina, inda suka sace mutane goma sha shida ciki har da Maigarin Kaigar Malamai, Kabir Mai Unguwa.
Majiyarmu ta tabbatar mana cewa ‘yan bindigar sun zo ne a tsakar daren shekaran jiya litinin, wayewar safiyar jiya talata, sun kwashe tsawon awowi suna harbe-harbe, sun jiwa wasu raunuka. Sun shiga gida-gida suna bincike bayan sun tsorata mu, sun tafi da Mai unguwar garin, sun tafi matan sure shidda da ‘yan mata da kuma yara kanana shidda.
A wani labarin kuma ‘yan bindigar a yankin karamar hukumar Jibia, inda suka yi awon gaba da wata motar haya, dauke da fasinjojin da ke ciki, akan hanyar Shimfida zuwa Gurbin Baure, har zuwa hada wannan rohoto ba’a tantance yawan su ba. Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce ana cigaba da bincike, kamar yadda wata kafar yada labarai ta tuntubi shi.

