Site icon Muryar 'Yanci

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kulle Mutane A Daki Sannan Suka Banka Musu Wuta

IMG 20240211 WA0197

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewa ‘yan taadda a karamar Hukumar Kankara sun sanya mutane a dakuna sun kulle sannan suka banka masu wuta suka kone.

Kamar Yanda Shugaban Kungiyar Yan Social Media na APC Karamar Hukumar Kankara( APC social media Kankara LGA) Mal Isah Abdullahi, ya kawo wani rahoto cewa, a garin unguwar baushe Yau talata 5)3)24 sun Shiga wannan gari inda suka kashe wasu suka sace wasu sannan suka danna Wasu mutane a daki suka banka masu wuta su ka kone.

Abinda yake faruwa a Karamar Hukumar Kankara ba duka kuke ji ba, Amma abun ya wuce kima, Wasu kauyukan yanzu sun Zama tarihi.

Exit mobile version