A ranar Talata ‘yan bindiga suka kashe mutum 14 a karamar hukumar Sabuwa dake jihar Katsina.
Lamarin ya afku ne sakamakon wani direban amalenke ya je debo yashi da keken shanunsa, inda ya yi karo da yan ta’adan suka kwance masa shanun da tsiya suka yi gaba da su
Hakan ne ya sa ‘yan gari suka bazama cikin dajin domin ganin barayin sun dawo da shanun amma abin ya gagara, wanda ya ja kashe mutum 14 ‘yan cikin gari da suka je kwato shanun.
Har aka gama gwagwarmayar, ba a sami shanun ba, kuma ba a kashe dan ta’ada ko daya daga cikin barayin ba.
Tuni aka yi masu sallar jana’iza a cikin garin Sabuwa gaba dayansu, a yau Laraba.

