Allah ya yi wa Alhaji Aminu Umar Radda rasuwa, sakamakon harbin da ‘yan bindiga suka yi masa a lokacin da suka je garin Radda, da ke karamar hukumar Charanchi, a jihar Katsina. Inda suka sace mai garin kuma yaya a gurin shi.
Alhaji Aminu Umar Radda, wanda yaya ne ga Shugaban Hukumar Kula Da Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i Na Nijeriya wato (SMEDAN) Dr. Dikko Umar Radda (Gwagwaren Katsina)
Majiyarmu ta tabbatar mata cewa bayan raunin da ya samu, aka kai shi wani asibiti a Kano, a can ya rasu.
A wani labarin kuma, ‘yan bindigan da suka sace maigarin na Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, sun sako shi bayan kwashe kwanaki a hannun su.
Allah ya jikansa da rahama!
Daga Jamilu Dabawa, Katsina

