Site icon Muryar 'Yanci

Katsina: Masari Zai Ciwo Bashin Biliyan 50

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta fara wani shiri na kar?o bashin Naira biliyan 50 domin yin wasu ayyuka a cikin shekarar 2021.

Kwamishinan kasafin ku?i da tsare tsaren tattalin arziki na Jihar Hon. Faruk Lawal Jo?e ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim ka?an bayan kammala taron majalisar zartaswar jihar a ranar Laraba.

Kamar yadda ya ce za a yi amfani da ku?in wajen kammala wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta fara.

Haka kuma, kwamishinan ya ce a zaman majalisar zartaswar an amince da Naira biliyan 283 a matsayin ?udirin kasafin ku?in shekarar 2021.

Kuna ganin Ciwo bashin makudan kudade ya dace a halin yanzu ga jihar katsina? Muna sauraran ra’ayoyin ku

Exit mobile version