Site icon Muryar 'Yanci

Katsina: Gwamnati Ta Kakabawa Matasa Biyan Harajin 2000 Duk Shekara


Gwamnatin Jahar Katsina ta amince kowane mazaunin jihar , da ya kai shekara goma sha takwas da ya rin?a biyan harajin naira dubu 2000 a duk shekara.

Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar, Faruq Lawal Jobe ne ya bayyana haka a ranar Larabar nan bayan kammala taron majalisar Zartaswar jahar.

Jo?e ya bayyana cewa haraji ya shafi ma’aikacin gwamnati da wanda ba ma’aikacin gwamnati ba, mai Sana’a da ma wanda baya sana’ ar, ?an jiha da ba ?an jaha ba duka ya wajaba a biya

Saidai a wajen Mata an ce sai mace mai aikin albashi, ita ce ka?ai za ta biya harajin.

Harajin dai wanda aka kira da “harajin raya kasa” kwamishinan ya ce an tsara yadda za’a rin?a karbarsa inda ya ce sun bullo da wani tsari da zai dauki bayanan yawan dukiya da hoto da katin kuria ko katin zama dan Kasa da lambar BVN da kuma wadanda ke makwabtaka da wanda ya biya harajin.

A ?angaren jangali kuma Jobe ya ce duk wanda ya mallaki shanuwa zai biya naira dari biyar a kan kowane sa ko shanuwa a duk shekara.

Exit mobile version