?ungiyar Arewa Decide 2023 sun yi tattaki tare da ha?in guiwar ?ungiyoyi 74 na PDP don wayar dakai a kan za?en Atiku Abubakar a matsayin shugaban ?asa a za?en shekarar 2023.
An rawaito cewa, tattakin ya wanzu ne a daide wurin tinin Liyafa har zuwa hedkwatar PDP dake a cikin ?waryar Katsina.
A nasa jawabin, Shugaban ?ungiyar reshen jihar Katsina, Comrade Kabir Umar Gambo, yace tattakin ya samu goyon bayan sama da ?ungiyoyi 74 na jam’iyyar PDP a Katsina.
Yace suna bi jiha-jiha ne a fa?in Arewacin Najeriya domin wayar da kan jama’a, tare da nuna nagartar Atiku Abubakar a matsayin shugaban ?asa.
Sannan yayi kira ga gwamnoni 5 na PDP da suka fan?are su dawo a ha?a kai domin a ciyar da ?asar nan gaba, yace kowanne gida ana iya samun rabe-raben kai bare jam’iyyun siyasa.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina, Alhaji Lawal ?an?aci, wanda ya samu wakilcin Ibrahim Galadima, ya nuna farin cikinsa game da ?ungiyar, duba da yadda take aiki tu?uru don ganin Atiku Abubakar ya kai ga gaci.
Tsohon ?antakarar Chairman na Katsina a jam’iyyar PDP Sanusi Audu Fari, yace lokaci yayi da za su yi waje da jam’iyyar APC a ?asar nan baki ?aya.
Yace idan kowa yayi tunani da ?walwar da Allah ya masa zai san cewa ci-baya ne aka samu ba cigaba ba a mulkin jam’iyyar APC.

