Site icon Muryar 'Yanci

Katsina: An Kama Dan Bindiga Mai Shekara 14

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan Jihar ta ce ta kama wani yaro ?an ?asa da shekara 20 da zargin shiga ayyukan ‘yan fashin daji da suka addabin yankin arewa maso yammacin ?asar.

A cewar kakakin ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, yaron mai shekara 14 ya amsa laifin kashe mutum biyu yayin wani hari da suka ta?a kaiwa.

“Yaron yana cikin wa?anda suka kai hari a Mallamawa cikin ?aramar Hukumar Jibia da kuma wasu a wajen Jihar Katsina, inda ya ce ya tuna lokacin da ya kashe mutum biyu,” in ji SP Gambo.

“Kuma ya shiga hare-haren da aka kai a Dankulumbo da Kukar Babangida, duka a Jibia. Sannan ya yi ?wacen shanu da ba a tantance adadinsu ba.”

Ba kasafai ake kama yara ?anana ba da zargin taimaka wa ‘yan fashin duk da cewa ‘yan sanda sun sha kama mata da kayayyaki a kan hanyarsu ta kai wa miyagun.

Har yanzu wasu sassa na jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Neja – inda ‘yan fashin suka fi addaba da kashe-kashe da satar mutane – na cikin ?aukewar layukan sadarwa, matakin da gwamnatoci suka ?auka da zummar da?ile ayyukan maharan

Exit mobile version