Site icon Muryar 'Yanci

Kashi 80 Na Wadanda Aka Kashe A Najeriya ‘Yan Arewa Ne – Bincike

Wata kididdiga game da sha’anin tsaro a Najeriya ya nuna cewa kashi 75.6 na mutanen da aka kashe sakamakon hare-hare a watan Yuni a arewacin kasar suke.

Sabuwar kididdigar, wadda kamfanin Beacon Consulting Limited da ke nazari kan harkokin tsaro ya fitar a wannan watan, ta bayyana cewa an kai hari 338 a fadin kasar a watan na Yuni lamarin da ya kai ga sace mutum 651.

Kazalika an kashe “mutum 765. Wannan lamari ya faru ne a kananan hukumomi 185 da ke jihohi 36 da Abuja, babban birnin kasar.”

Alkaluma kan lamarin sun bayyana cewa kashi 28.6 na kashe-kashen sun faru ne a Arewa maso Gabas ( an kashe mutum 219 ), kashi 23.5 a Arewa ta Tsakiya ( inda aka kashe mutum 180), kashi 23.5 a Arewa maso Yamma (mutum 180 sun mutu).

Kazalika kashi 10.5 na kashe-kashen ya faru ne a Kudu maso Yamma ( an kashe mutum 80), yankin Kudu maso Gabas na da kashi 9.2 (an kashe mutum 70) da kuma Kudu maso Kudu mai kashi 4.7 (an kashe mutum 36).

Exit mobile version