Site icon Muryar 'Yanci

Kashe Shekau: ISWAP Ba Ta Cancanci Tukwici Ba – Amurka

?asar Amurka ta bayyana cewa ?ungiyar ISWAP ba zata samu ko sisi ba daga cikin dala miliyan $7m data sa kan duk wanda ya gano inda Abubakar Shekau yake.

Yayin da take martani kan rahoton mutuwan shugaban maya?an Boko Haram ?in, Amurka tace ba zata baiwa ?ungiyar dake ?ar?ashin ISIS ba ko sisi.

Wannan na ?unshe ne a wani rubutu da sashin shari’a na ?asar Amurka yayi a shafinsa na Tuwita @RFJ_USA, rubutun ya bayyana cewa: “Rahoton da muka samu yau ya nuna cewa shugaban ?ungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya kashe kansa a wata fafatawa da suka yi da maya?an ISWAP dake biyayya ga ISIS.”

“Baku cancanci tukuicin da muka sa ga wanda ya bada bayanan inda yake ba, haka shirin namu ya ?unsa.”

Ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Yuni, 2012, sashin shari’a na ?asar Amurka ya bayyana shugaban ?ungiyar Boko Haram, Abubakar She?au, a matsayin ?aya daga cikin yan ta’addan duniya.

Bayan shekara daya da saka sunan Abubakar Shekau, sashin ya sanya tukuicin dala miliyan $7m ga duk wanda ya kawo bayanan inda ma?oyarsa take.

Exit mobile version