Kungyar ?arkashin shugabanta Ajaero ta bayyana cewa ba ta cimma matsaya ba game da yarjejeniyar ?arancin albashi da kuma rage tsadar wutar lantarki da ake fama da shi a ?asar.
A zaman taron da muka yi, babu gwamna ko ?aya da ya halarci taron, haka kuma babu wani minista in banda ?aramar ministar Kwadago Nkiruka Onyejiocha.
Haka nuni cewa maganar ?arin albashin ba ta ?a?a su da ?asa ba ko ka?an, ba ita ce a gaban su ba.
Kungiyar ta ce tunda gwamnati ba ta ga amfanin zaman ba, suma za su nuna wa gwamnati cewa lallai sai sun tilasta ta ta yi abinda ya dace, wato ta ?ara albashi da rage wutar lantarki.
Kungiyar kwadago ta ce lallai a dawo da ku?in wutar lantarki baya, wato kamar yadda yake a da can.
Ta gudanar da zanga-zanga amma gwamnati ta yi biris da ita.
Mu fa talakawa ne a gaban mu, ba zamu yi ?asa a guiwa ba har sai mun tilasta gwamnati ta yi wannan ?ari sannan kuma wutar lantarki ya koma yadda yake a baya.
Wannan shine matsayar mu muma babu gudu ba ja da baya, yajin aiki za a fara shi. Saboda haka gwamnati ta kwan da shiri. Kuma ba za a janye ba sai an biya mana bu?atun mu duka.

