Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gamayyar ?ungiyoyin ?wadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Gamayyar ?ungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma’a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin.
A farkon makon nan ne dai manyan ?ungiyoyin ?wadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ?an?anta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.
Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.
Su ma ?ungiyoyin ?wadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ?an?anta.

