Site icon Muryar 'Yanci

Karancin Albashi: Gwamnonin PDP Sun Goyi Bayan Kungiyar Kwadago

IMG 20240229 WA0092

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnoni wa?anda aka za?a a ?ar?ashin inuwar Jam’iyyar PDP sun bayyana goyon bayansu ga ?ungiyar ?awadago ta ?asa a yun?urin da take yi na ganin gwamnatin Najeriya ta yi ?ari a albashin ma’aikatan ?asar mafi ?an?anta.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a sanarwar ?arshen taro da suka fitar a bayan taron su na ?asa da suka gudanar a jihar Enugu, da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Yayin da suka koka kan tafiyar hawainiyar da tattaunawar gwamnati da ?ungiyar ?wadago ke yi, gwamnonin sun yi la’akari da cewa matsayar da ?ungiyar ta ?auka ya dace a halin yanzu ganin irin wahalhalun da ?an Najeriya ke ciki sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Sanarwar ta ?ara da cewa ”Yayin da taron gwamnonin ke goyon bayan bu?atar ?ungiyar ?wadago, dole ne duk wata yarjejeniya ta yi la’akari da albashin da gwamnatocin ?ananan hukumomi da na jihohi za su iya biya”.

”Yayin da ake ci gaba da tattaunawa, muna kira ga dukkan ?angarori da su kai zuciya nesa, kar a kai ga furuci da kuma ayyukan da za su iya haifar da karya doka, wanda ka iya kai wa ga jefa tattalin arzi?i cikin ru?ani.”

Gwamnonin na PDP sun kuma bayyana takaici kan “yadda tsare-tsaren gwamnatin tarayya ?ar?ashin jam’iyyar APC ke neman gurgunta tartalin arzikin ?asar.”

Exit mobile version