Shugaban Majalisar Malamai ta ?asa, Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya she?a zuwa Jam’iyar ADC.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ?arshen 2021 ne Sheikh Khalil ya baiyana ficewar sa da ga Jam’iya mai mulki ta APC amma bai baiyana wacce ya koma ba.
Sai dai kuma a yau Juma’a ne Sheikh Khalil ?in ya baiyana ADC a matsayin jam’iyyar da ya koma.
Bayanin komawa jamiyyar ADC da malamin ya yi, na kunshe cikin wani sako da shugaban jamiyyar na jihar Kano, Shuaibu Ungoggo, ya gabatar ga manema labarai.
Cikin bayanin na sa, Shuaibu Ungoggo, ya ce malamin ya shigo jamiyyar ta su ta ne tare da Dakta Saidu Ahmad Dukawa na jamiar Bayero, da kuma wasu malaman jamia guda takwas da su ka rufa masa baya, a kokarinsu na ganin cewa an ceto jihar Kano daga halin da ta ke ciki.
Ya kuma baiyana cewa nan gaba kadan zaa shirya taron karbar Sheikh Khalil a jamiyyar.

