Site icon Muryar 'Yanci

Kano: Shugaban Majalisar Malamai Ya Fice Daga APC

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Shahararren malamin addinin musulunci a jihar kuma Shugaban majalisar Malamai ta Jihar Malam Ibrahim Khaleel, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.

Shehin Malamin ya shaida wa jaridar Dailytrust cewa ya rubuta takardar murabus daga APC duk da har yanzun bai mi?a ta ga shugabannin jam’iyya ba. Ya ?ara da cewa dalilin da yasa bai mi?a takardar murabus ?in ba shi ne saboda rikicin dake faruwa a APC reshen Kano, wanda a yanzu yake gaban kotu, ana buga shari’a.

“Na rubuta takardan murabus ?ina daga jam’iyyar APC kuma ina jiran hukuncin da kotu zata yanke kan rikicin shugabanci dake faruwa tsakanin ?angarori biyu.” “A wannan lokacin zan mika takardar murabus ?ina ga shugabannin da aka tabbatar.”

Malamin ya ?ara da cewa ya so ficewa daga jam’iyyar tun a watan Nuwamba, amma da majalisar malamai ta jihar Kano ta saka baki ne ya ja hankalinsa ya fasa.

Sheikh Khaleel ya bayyana cewa ba zai fa?i ainihin abin da yasa ya ?auki matakin fita daga jam’iyyar ba ko kuma jam’iyyar da zai koma ba.

Exit mobile version