Babbar jamiyyar hamayya ta PDP tayi karar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) saboda sanya su cikin kunshin jamiyyun da za su shiga zaben kananan hukumomin jihar.
Shugaban jamiyyar na jihar Kano Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan, yayin da yake tattaunawa da manema labarai a birnin Kano.
Sagagi wanda shi ne shugaban tsagin jamiyyar a Kano, ya ce tuni suka dauki matakin gabatar da hukumar KANSIEC din gaban kotu.
Wada Sagagi ya kara da cewa babbar kotun tarayya ta tabbatar da shi a matsayin shugaban jamiyyar, sabanin daya shugaban tsagin PDP bangaren Aminu Wali, wato Muhammina Lamido.
Jamiyyar ta kuma jaddada matsayar ta na cewar baza ta shiga cikin zaben kananan hukumomin ba, da zai gudana a ranar 16 ga watan Janairu da muke ciki.
Tuni dai shugabannin Jamiiyya PDP tsagin tsohon gwamna Kwankwaso suke ta bada sanarwar cewa ba za su shiga cikin Zaben kananan hukumomin ba, ya yin tsagin Aminu Wali ke cewa su suna cikin zaben.

