Site icon Muryar 'Yanci

Kano: Mawakin Da Ya Yi ?atanci Ga Annabi Ya Nemi Gafarar Musulmi

Jami’an hukumar ta DSS sun shaida wa wakilin BBC a Kano cewa mawakin ya “nemi afuwar al’ummar jihar da daukacin Musulmin duniya kan wakar da ya yi”

Kazalika, mahaifan matashin sun yaba wa DSS da hukumar tace fina-finai bisa ga wannan mataki da suka dauka.

A watan Agustan 2020 wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wani matashi Yahaya Aminu Sharif, mai shekara 22, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ?atanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

Tun a watan Maris na shekarar ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ?waryar birnin Kano ya yi wata wa?a, wadda aka zarge shi da yin ?atancin a cikinta.

Hakan ya sa matasa sun yi zanga-zanga a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda suka nemi a hukunta shi.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa sun far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai kuma suka lalata duk abin da ke ciki.

Exit mobile version