Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar malaman Jamiar Bayero sun koma bakin aiki a ranar Litinin bayan kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta sanar da janye yajin aikin da suka shafe wata takwas suna yi.
Dalibai da maaikata sun fara shiga jamiar a ranar Litinin inda suka bayyana farin cikinsu tare da fatan za a fara daukar darasi.
Kungiyar dai ta ce ta rubuta wa hukumar jamiar Bayero Kano cewa malaman sun dawo bakin aiki.
Yayin da malaman jamiar suka janye wannan yajin aiki, ga alama, shirye-shirye sun kankama na ci gaba da daukar darasi a jamiar Bayero Kano.

