Wata Babbar Kotu a Kano ta bu?aci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya biya jaridar Daily Nigeria ta Jaafar Jaafar da kamfaninsa Penlight Media Ltd diyyar N800,000 kan ba ta lokacinsu da kuma ?ata suna.
Labarin da jaridar Daily Nigeria ta wallafa a shafinta ranar Talata ta ce “kotun ta yi watsi da bu?atar da lauyoyin Ganduje suka gabatar a ranar 28 ga Yunin 2021, suna neman a dakatar da shariar ba tare da bayyana dalilai ba.
Lauyan Daily Nigeria Muhammad DanAzumi ya ?alubalanci bu?atar inda ya nemi kotun ta yi watsi da ita tare da bayyana ikirarin na Ganduje a matsayin marar tushe, in ji jaridar.
Ta kuma ce mai sharia S. B .Namalam ya umarci gwamnan ya biya Jaafar naira 400,000 haka kuma kamfaninsa N400,000 kan ?ata suna.
A 2018 ne Jaridar Daily Nigeria ta wallafa bidiyon da ke ikirarin nuna gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana soke daloli a aljihunsa, kan zargin kar?ar rashawa, zargin da gwamnan ya ?aryata.

