Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Wata kotu a birnin ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari
Danbilki zai cigaba da zama a gidan yari har zuwa 15 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura alumma.
Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jamiyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jamiyyar APC na jihar Kano.

