Wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar ciyo bashin naira biliyan 10 domin sayen kamarorin CCTV.
Kotun da alkali Abdullahi Muhammad Liman ke jagoranta ta ce bata amince a ciyo wannan bashi ba tare da umarta dole a bi umarninta.
Wata kungiya ta Kano First Forum (KFF), ce ta shigar da kara, tana neman kotu ta hana gwamnan Kano ciyo wannan bashi.

