Labarin dake shigo mana daga birnin Kano Jalla babbar Hausa na bayyana cewar Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ce kusan kaso 70 cikin dari na sabbin gine-ginen da aka yi a filin Kwalejin Fasaha ta Kano mallakin Gwaggo ne matar tsohon gwamna jihar Abdullahi Umar Ganduje da yayanta
Gwamna Abba Gida-Gida ya ce nan ba da jimawa ba za a fara fidda sunayen wadanda aka mallakawa dukiyar alummar Kano kowa ya gani.
Lamarin rusau a Kano dai wani al’amari ne da ya ?auki hankalin ‘yan Najeriya, lamarin da wasu ke ganin dacewar sa yayin da wasu ke ganin akasin haka.

