Site icon Muryar 'Yanci

Kano: Jagorar Masu Zanga-Zanga Ta Mika Wuya

?aya da ga cikin jagororin zanga-zangar #NoMoreBloodshed in Kano state, Zainab Naseer Ahmed ta nisanta kan ta daga zanga-zangar, jim ka?an bayan ta dawo daga ofishin ?an sandan farin kaya, DSS.

DSS ?in ne dai su ka gaiyace Zainab domin tambayoyi sakamakon sa hannun ta a zanga-zangar da a ka ha?a a wasu jihohin arewa domin jawo hankalin gwamnati a kisan gillar da a ka yi wasa wasu matafiya 42 a Sokoto.

Bayan ta shafe wajen awanni biyu a hannun DSS ?in, sai gani a kai Zainab ta wallafa a shafin ta na facebook cewa ta zare hannun ta daga zanga-zangar.

“Ina son mutane ku sani cewa daga yau na zare hannuna daga zanga-zangar da a ka fara yau, ina son kowa ma yayi haka.

“Na san akwai wasu abubuwa kuma na damu da zaman lafiyar alumma kuma bana son wani ya samu rauni ko jikkata.

“Gaskiya ha?ari ne yin zanga-zanga yanzu a Kano saboda rahoton da na samu ya nuna cewa wasu ?atagari na nan ma shirin amfani da zanga-zangar domin kawo tarzoma,”

“Ina mai baku shawarar da ku yi zaman ku a gida domin “zaman lafiya ya fi zama ?an sarki”,

Exit mobile version