A ranar Jumaa ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar gwamna na jamiyyar PDP a jihar Kano.
An rawaito cewa, jamiyyar PDP ta jihar ta rabu gida biyu, inda ko wanne bangare ya gudanar da zaben fidda gwani na jamiyyar wanda ya haifar da Mista Wali da Muhammad Sani-Abacha dan marigayi shugaban mulkin soja a matsayin yan takarar gwamna.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bangaren Shehu Sagagi da ya gabatar da Mista Sani-Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jamiyyar a jihar.
Sai dai a wani yanayi na daban, ofishin na INEC na Kano a yau Jumaa sai ya fitar da sunan Wali tare da abokin takararsa, Yusuf Dambatta a matsayin yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaben 2023.
Abba Kabir-Yusuf, wanda ke daga tutar jamiyyar , NNPP, shi ma ya shiga jerin sunayen tare da abokin takararsa, Aminu Abdulsalam.
Haka shima ?an takarar gwamna a jam’iyar PRP, Salihu Tanko Yakasai, sunansa ya fito.
Sannan Sheikh Ibrahim Khalil, ?an takarar gwamna a jam’iyar ADC, yana cikin jerin sunayen.

