Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamiti mai ?arfi wanda zai tabbatar da ragin kashi 25% na ku?in makarantun ku?i a jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar Muhammad Said ?iru ya ?addamar da kwamitin ranar Alhamis, a ofishinsa da ke Kano.
Wata sanarwa da ta fito daga jamiin hud?a da jamaa na maaikatar ilimin, Aliyu Yusuf ta ce Kwamishinan ya bu?aci wakilan kwamitin su tabbatar da makarantun sun yi biyayya ga umarnin gwamnati na rage ku?in zangon karatu na uku.
Iyaye da dama sun koka akan yadda kudaden makaranta ke hauhawa duk bayan zango Wanda iyaye da dama basa iya daukar nauyi musamman sakamakon bullar annobar korana data addabi tattalin arxikin duniya.
Ya kuke kallon wannan mataki da gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya dauka a wannan lokaci?
Ku kasance da mu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su.

