Site icon Muryar 'Yanci

Kano: Ban San Wanda Zan Mika Wa Mulki Bayan Kammala Wa’adina Ba – Ganduje

Gwamnan Jíhar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Allah ne kadai yasan wanda zai mika wa ragamar mulkinsa ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara.

Gwamna ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke kaddamar da sabbin hanyoyi a jihar.

Idan ba a mantaba jam’iyya mai ci ta APC a jihar ta maka Hukumar Zabe da kuma jam’iyyar NNPP a kotu bisa zargin tafka magudi lokacin zaben gwamnan jihar da ya gabata a watan Maris na wannan shekara.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

A watan Afrilu da ya gabata ne gwamna Ganduje ya kafa kwamitin mutum 17 daga ma’aikatu da dama don mika mulki ga sabon zababben gwamnan jihar. Sannan kwamitin na da karin mamabobi 100 don taimaka musu wurin mika mulki cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

Exit mobile version