Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Ganduje ya fara shan suka kan taka hoton wanda ya gada kuma madugun kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso lokacin taron APC wanda ya gudana a birnin Kano.
Da yake jagorantar gangamin ranar demokara?iyya 12 ga watan Yuni, inda ya karbi wasu da suka sauya she?a zuwa APC a filin wasan Kano Pillars, gwamna Ganduje ya sa ?afa ya take hoton kwankwaso.
Amma gwamnan yana shan suka daga wurin al’umma ta ko’ina kan wannan matakin da ya ?auka na take hoton.
Daya daga cikin masoyan gwamnan kuma tsohon kwamishin ayyuka na jihar Kano, Mu’azu Magaji, ya nuna cewa abinda gwamnan yayi ba dai-dai bane. Yace: “A’a mai girma gwamna a’a, duk wanda ya baka wannan shawarar a matsayin adawar siyasa to baisan mecece siyasa da abinda ta ?unsa ba.”
“Kayi hakuri yallabai, amma abinda kayi ba dai-dai bane a matsayinka na yayan mu kuma shugaban mu. Koma dai menene Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan Kano ne, kuma tsohon minista a Najeriya.” “Kayi tunanin yadda zamu ji idan hakan ta faru da kai bayan ka gama mulkin ka kabar ofis ?in gwamnan Kano.”
Wani da ya fa?i ra’ayinsa kan wannan lamarin, Muhammad Jamu, yace: “Wannan abun kunya ne ace mutum mai daraja kamar Ganduje ya ?auki wannan a matsayin adawar siyasa, ya taka hoton mai girma shugaban cigaban Ilimi, Rabiu Musa Kwankwaso.” “Wanda shine mutumin da ya yi sanadinsa zama abinda ya zama a yanzun.
Sa?o na gareka (Ganduje) a bayyane yake, duk abinda kake gani a yanzun wataran zai wuce. Ina addu’a Allah ya kaimu lokacin da wa?anda ke baka irin wannan shawarar zasu koma suna ya?i da kai.”
“Har mabiya jam’iyyar APC zasu tabbatar da cewa duk wanda ya bada umarnin aikata haka ba ?wararre bane, baima san abinda yake ba.” “Ganduje, adawar ka ga kwankwaso ce zata cinye maka lokacinka, ka zama gwamna shekara 6 da ta wuce amma mutumin nan ya fika masoya na ha?i?a, yan a?ida.”

