Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin Ganduje tace duk wani mamban jam’iyyar APC dake neman wani mukamin jam’iyya sai ya yi gwajin shan miyagun kwayoyi.
Kwamishinan ya?a labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Kano.
Kwamishinan ya shawarci dukkan yan takara da su je ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ranar Talata da misalin ?arfe 7:00 na safe domin gudanar da bincike a kansu.
Bugu da ?ari, Kwamishina yace sai da aka gudanar da makamancin irin wannan gwajin ga yan takara a za?en shugabannin ?ananan hukumomi. Hakanan sai da aka yiwa duk wani mai rike da mukamin siyasa na jiha, da ya ha?a da mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kano, kafin a basu ofishinsu.
Garba ya ?ara da cewa tuni gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya sanar da hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin. Ya kuma yi garga?in cewa gwamnati zata ?auki mataki kan duk wanda ta gano yana ma’amala da wasu haramtattun kwayoyi kuma ba kan ?a’ida ba.
Garba yace yayin za?en shugabanni a matakin ?ananan hukumomi, a?alla yan takarar kansila 13 aka dakatar, kuma aka maye su da wasu bayan gwajin NDLEA ya bayyana suna ma’amala da kwayoyi.
“Wannan gwamnatin ta shirya sosai wajen ya?i da safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da kwaya ba bisa ?a’ida ba.”

