Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ?ar?ashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar da ta hana ?an adaidaita-sahu bin wasu manyan tituna cikin kwaryar Kano.
Shugaban Hukumar kula Da Zirga-zirgar Ababen-hawa, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Kano.
Ya ce an janye dokar ne saboda matu?a baburan adaidaita-sahu ?in sun yi biyayya kuma al’umma sun yi suka a kan dokar.

